YANDA AKE YIN ALKAKI

ALKAKI RECIPE “YANDA AKE YIN ALKAKI

1. Alkama mudu ďaya
2. Sugar gwangwani 6
3. Nono na shanu
4. Ɗanƴen Nan Shanu
5. Butter simas rabi
6. Mai kwalba biyu
7. Lemon Tsami Cokali 2
8. Kanwa

PROCIDURE “HANYAR DA AKE BI”
Za’a cire dukkan dattin dake jikin Alkama, sannan a wanke a baza ta a rana ta bushe. Sai a kai Injin niƙa a niƙa ta, amma ba niƙan laushi ba  ɓarzawa ake yi, idan kun yiwa masu niƙan bayani sun san yanda za su niƙa mu ku.

Idan aka dawo da niƙan a bude tsakiyar Alkamar a kwanon kwaɓi sannan sai a juye Nonon shanu, butter, man shanu, sai a mix ɗin shi sosai har sai ya hade. Sai a zuba ruwa amma mix ake masa mai qarfi da gaske yanda zai hade da kyar, Sai a rufe a barshi ya kwana.

Idan an  tashi da safe sai a  jiqa kanwa, a rinqa yayyafa masa ana haɗashi ana bugawa. Har sai kun ɗiba a hannun ku kun masa naɗin Alkaki kun ga bai karye ba. Wato kun yi tsaho dashi kun murza duka bai karye ba. Dan haka ba ƙaramin bugu za ku yi masa ba. Ba a jibga masa ruwa, yayyafa masa kawai za ku rinƙa yi kuna buga shi.

Sai a zuba sugar a Tukunya, a zuba ruwa kofi uku a ɗaura a wuta, sannan a zuba Cokali ɗaya na Leman tsami, hakan zai zai kuga Sugar har ɗiga yake a jikin Alkakin, amma idan ba kwa buƙatar haka too kada ku saka gaba ɗaya.

Wajen dafa sugar a kula yana fara yin kumfar farko na dahuwa a ɗiba a cokali yana ɗan fara shan iska zaku ga yayi danqo. Sai a sauke. Sannan wajen soya Alkakin a saka mai aƙalla kwalba biyu ko sama da hakan ma, baya shan mai amma yana buƙatar mai wajen soya shi, Kuma kada a hura wuta mai yawa kaɗan-kaɗan yanda cikin zai soyu.

Bayan kin tsane shi a mai kai tsaye cikin sugar za a saka shi, idan kuna gabda tsamewa sai ku kwashe na cikin sugar ku sa a kwanon da zaku ajiye. A kula, Ludayin da za ku dunga Amfani da shi wajen suya to zamto daban da wanda za ku dunga amfani da shi a wajen yin amfani da Sugar.

Kalli Video

Mai da martani